
"Kamar yadda kasan cewa dole ne ka mutu, to dole a sake tayar da kai a bayan mutuwar taka domin ayi maka hisabi, to sai ka kyautata aiyukan ka domin ka sami sauƙin hisabin a gurin buwayayyen sarki Allah ta'ala"
-
"Za mu ridudduge za'a mayar damu ƙasusuwa a bayan mutuwarmu, zamu zamto tamkar ba'a taɓa yin tarihin mu a ban-ƙasa ba, mu ba komai bane face bayin Allah gajiyayyu, Allah shi ne yake da ikon yin duk abin da yaga damar yi damu a rayuwarmu ko a bayan mutuwarmu, to me yasa wasun mu suke ɗaukar kansu tamkar sunfi kowa? me yasa wasu daga cikin mu suke nuna ji-ji da-kai da nuna ɗagawa ga wasu? me ya sa sashin mu yake zaluntar sashin mu? me yasa wasu mutanen suke jin cewar kamar in sun mutu babu damar sake tayar dasu balle ayi musu hisabi?"
-
"Lallai ne haƙiƙa Allah yana da ikon sake tayar damu bayan mutuwarmu, kuma sai ya tambaye mu abisa duk abin da muka kasance muna aikatawa a wannan duniyar, kuma tabbas babu wani gwani mai iya bayar da labarin abin da bayi suke aikatawa a wannan duniyar kamar Allah"
Ismail Smart Alpholtawy.
Alpholtawy.
My Written Text Color.