1644227197-picsay
HomeBlogAbout Me

HAKKIN MACE AKAN MIJINTA 01

Musan Hukumcin Addininmu

Yaku bayin Allah wadannan hakkokin kiyaye su shi ne kashin-bayan tabbatuwar aure da ni’imarsa, rashin kiyaye su kuwa babbar matsala ce. Ga su nan kamar haka:

(1) Samar mata da wurin zaman da ya dace don kare mutuncinta, kamar yadda Allah (SWT) Yace:

أَسْكِنُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ سَكَنْتُمْ مِنْ وُجْدِكُمْ وَلَا تُضَارُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُوا عَلَيْهِنَّ ۚ

( Ku zaunar da su a inda kuke zaune gwargwadon samunku)

(2) Dole ne ya sama mata abinci gwargwadon karfinsa, kamar yadda Allah (SWT) Yace:

لِيُنْفِقْ ذُو سَعَةٍ مِنْ سَعَتِهِ ۖ وَمَنْ قُدِرَ عَلَيْهِ رِزْقُهُ فَلْيُنْفِقْ مِمَّا آتَاهُ اللَّهُ ۚ

( Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuma aka kuntata masa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi)

(3) Ya tufatar da ita a lokacin da ya dace, gwargwadon halinsa, Manzon Allah SAW yace: “Ka tufatar da ita, idan ka tufatar da kanka.” (Abu Dawud 2142, Ibnu Majah 1850).

(4) Biya mata bukatarta ta ‘ya mace wannan dole ne, gwargwadon yadda Allah (SWT) Ya halicce su, haka zai taimaka wajen tsare mata mutuncinta, kuma hakki ne babba, kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Lallai ga iyalinka akwai hakkinta a kanta” (Bukhari 1977, Muslim 1159).

Duk wanda yake tare da matarsa, har ya kaurace mata tsawon wata 4 babu saduwa, sai ta yi kararsa wajen magabata, ko ya sake ta, ko ya dawo ya gyara hali, wannan ai cutarwa ce babba.

(Wannan shi ake kira Iyla’i, kamar yadda ayoyin Bakara suka yi bayani, duba bayanin malamai a cikin ‘Alfikhu Alal Mazahibil Arba’ah’ na Abdurrahman Aljuzairy).


الله تعالى أعلم


ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE
Apholtawy

Ismail Hussaini Adam

Ismail Smart Alpholtawy.

Katsinawa Dukawa

Alpholtawy.

This is The Styles

My Written Text Color.


XtGem Forum catalog